Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMET) ta fitar da hasashen yanayi na kwana uku, daga Litinin 21 zuwa Laraba 23 ga Yulin 2025, inda ta bayyana cewa za a samu ruwan sama da iska mai ƙarfi a sassa daban-daban na ƙasar.
A kan haka NiMet ta shawarci al’umma da su yi taka-tsantsan kan yiwuwar samun ambaliya da kuma ɓarna da iska mai ƙarfi ke iya haddasawa.
A cewar sanarwar da hukumar ta wallafa a shafin sada zumunta na X, jihohin Arewa da na Kudu da kuma yankin tsakiya, duk za su fuskanci iska mai ƙarfi haɗe da ruwan sama.
Hasashen ya nuna cewa a ranar Litinin da safe, an samu ruwan sama da iska a jihohin Taraba da Adamawa da Kebbi da Borno da Yobe da Gombe da Bauchi da Sokoto da Kaduna.
Ya kuma nuna cewa yankin tsakiyar kasar kamar Abuja da Niger da Plateau da Nasarawa da Benue da Kogi su ma za su samu ruwan sama daga rana zuwa yamma.
Ranar Talata da safe kuma ana sa ran ruwan sama da tsakar rana a Abuja da Kwara da Niger da Plateau.
A ranar Laraba da safe kuma, za a samu iska mai ƙarfi da ruwa a Katsina da Kano da Bauchi da Sokoto da Taraba sannan daga baya za a samu a Yobe da Jigawa da Kaduna da Borno da kuma Kebbi.