fidelitybank

Za a yi kwanaki 3 a na ruwan sama a Najeriya – NIMET

Date:

Hukumar kula da yanayin samaniya ta Najeriya (NiMet), ta yi hasashen samun ruwan sama kamar da bakin ƙwarya gami da tsawa daga yau Talata har zuwa ranar Alhamis a fadin ƙasar.

Hasashen yanayin da NiMet ta fitar a Abuja ta ce, akwai yiwuwar samun yanayin hadari mai ƙarfi a ranar Talata da kuma raguwar hasken rana a yankin arewacin ƙasar.

Hasashen, ta kuma ce ana iya samun ruwan sama da tsawa da safe a wasu jihohin arewa kamar Adamawa da Taraba da Sokoto da Zamfara da Katsina da Kebbi da kuma Kaduna,

Sannan da rana, mai yiwuwa za a yi ruwan sama da tsawa a sassan jihohin Bauchi da Gombe da Adamawa da Taraba da Kaduna.

A jihohin Kudu da na kusa da teku kuma, mai yiwuwa za a yi ruwa da tsawa da safe a jihohin Osun da Oyo da Ekiti da Ogun da Legas da Akwa Ibom da Ribas da Bayelsa da kuma Cross River.

A ranar Laraba, yankin arewa zai iya fuskantar baƙin hadari da dusashewar hasken rana inda hukumar ta yi hasashen samun ruwa da tsawa da safe a sassan jihohin Adamawa da Taraba da kuma Gombe.

www.legitnews.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp