Maimartaba Sarkin Ningi da ke jihar Bauchi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya, ya rasu, yana da shekara 88.
Sakataren masarautar, Alhaji Usman Sule, Magayakin Ningi, shi ne ya bayyana labarin rasuwar a wata sanarwa, inda ya ce, Allah Ya yi wa Sarkin rasuwa ne yau Lahadi da Asuba a Kano.
Sanarwar ta kara da cewa za a yi jana’izar Sarkin mai daraja ta daya, yau da karfe hudu na yamma a fadarsa da ke Ningi.
Bayanai sun nuna cewa ya rasu ne, a wani asibiti a Kanon, kwana biyu bayan ya dawo Najeriya daga Saudiyya inda ya je domin duba lafiyarsa.
An haifi marigayi Alhaji Yunusa Danyaya a shekarar 1936, a garin Ningi kuma ya zama sarki a shekarar 1978.