fidelitybank

Za a yi jana’izar sarki Olubadan na 42

Date:

Anjima a yau Juma’a ne za a yi jana’izar sarki Olubadan na 42 a birnin Ibadan da ke jihar Oyo.

Sarki Olubadan na Ibadan, Oba Olalekan Balogun ya mutu ƴan kwanaki bayan ya yi bikin cikarsa shekara biyu kan karaga.

Kakakin Sarkin, Dele Ogunsola ne ya tabbatar da mutuwarsa a ranar Alhamis.

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde shi ma ya tabbatar da mutuwar sarkin yana shekara 81 a wata sanarwa da ya fitar.

Gwamna Makinde ya bayyana cewa sarkin wanda shi ne Olubadan na 42 ya mutu ne a asibitin koyarwa na jami’ar UCH da ke jihar Oyo a kudu maso yammacin Najeriya.

Gwamna Makinde ya bayyana sarkin a matsayin mutumin da ya cimma nasarori da dama da suka zama ci gaba ga Ibadanland cikin shekara biyun da ya yi yana mulki.

“Babban bango ya faɗi; Sarki Dakta Balogun ya rasu,” in ji gwamna Makinde.

Kola Balogun, wanda ƙani ne ga sarkin ya ce za a yi jana’izar sarkin a gidansa da ke Aliiwo, kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Wane ne marigayi Sarki Olubadan na 42?

Marigayi sarki Oba Olalekan Balogun ɗan siyasa ne, ɗan kasuwa kuma tsohon sanata.

An haife shi a Balogun cikin watan Oktoban 1942.

Balogun ya taɓa zama mamba a hukumar gudanarwar manyan kamfanoni da dama a Najeriya da ƙasashen waje, musamman a ɓangaren man fetur da noma da kasuwanci da shugabanci da yawon buɗe ido.

Ya kuma taɓa riƙe muƙamai da dama a kamfanin mai na Shell.

Ya yi karatu a jami’ar Columbus International da jami’ar Brunel da kuma jami’ar Manchester – dukkansu a Birtaniya.

A fagen siyasa, Balogun tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ne a Najeriya a ƙarƙashin jam’iyyar SDP.

Ya kuma taɓa yi wa PDP takarar gwamna a jihar Oyo.

Daga bisani, Balogun ya zama sanata a Najeriya. In ji BBC.

daily post nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp