Za a yi jana’izar wadanda harin coci ya rutsa da su a majami’ar St Francis Catholic Church Owo, jihar Ondo da aka yi wa kisan gilla a ranar 5 ga watan Yuni a wannan makon, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya wallafa a ranar Talata.
Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan ta’adda ne sun kai farmaki cikin cocin kwanaki tara da suka gabata, inda suka kashe sama da mutane 40, tare da jikkata wasu da dama. Tuni dai ‘yan Najeriya da suka hada da shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin jihohi da dama suka yi Allah-wadai da wannan kisan kiyashi da aka yi a kasar.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, cocin Katolika na Ondo ta ce za a gudanar da jana’izar gamayyar mutanen da aka kashe a ranar Juma’a 17 ga watan Yuni.
Daraktan Sadarwa na zamantakewa na Diocese na Ondo, Revd. Uba Augustine Ikwu ya shaida wa gidan talabijin na Channels a Akure cewa za a yi jana’izar jama’a ne a wata sabuwar makabartar da ke kan titin Emure-Ile a garin Owo.
“Taron ya amince da cewa dukkan Gwamnonin su ba da umarni a sauke tutoci kasa-kasa a dukkan gine-ginen jama’a da gidajen gwamnati a fadin Jihohin Kudu maso Yamma, domin girmama wadanda harin ta’addancin Owo ya rutsa da su.