fidelitybank

Za a yi jana’izar ƴan wasa da ma’aikata 19 na jihar Kano da suka mutu bayan sun dawo daga wasan ƙasa

Date:

Motar da ke ɗauke da ƴanwasan Kano da masu horar da su a gasar wasanni ta ƙasa wato National Sport Festival ta Najeriya ta yi hatsarin a hanyar komawa gida, inda rahotanni suka ce mutum 19 daga cikinsu sun rasu, sannan wasu sun jikkata.

Lamarin ya faru kimanin kilomita 50 zuwa Kano a yau Asabar bayan motar ta taso daga jihar Ogun da ke kudu maso yammacin ƙasar bayan an kammala wasannin a ranar Juma’a.

Ibrahim Umar Fage shugaban riƙo na hukumar wasanni ta jihar Kano ya tabbatar wa BBC da aukuwar lamarin, inda ya ce, “ƴanwasanmu sun kwana a Abuja ne da safe sai suka kama hanyar komawa gida. A kusa da Dakatsalle suka yi hatsari. Motar ta faɗa wata gada da ke kusa da Ciromawa. Aƙalla mutum 19 zuwa 20 ne suka rasu, akwai wasu kuma a asibiti,” in ji shi.

Shi ma Kwamishinan matasa da wasanni na jihar, Mustapha Rabiu Kwankwaso ya bayyana kaɗuwarsa kan hatsarin, inda ya ce lamari ne da ya taɓa jihar baki ɗaya.

A wata sanarwa da kwamishinan ya fitar, ya ce “wannan lamarin abin tayar da hakali ne matuƙa. Muna jajanta wa ƴanuwa da iyalan waɗanda suka rasu da ma mutanen jihar Kano baki ɗaya,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa gwamnati za ta ɗauki ɗawainiyar kula da sauran waɗanda suka ji raunuka.

daily post

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp