Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya, NiMet ta yi hasashen cewa za fuskanci hasken rana da kuma hazo daga ranar Juma’a zuwa Litinin a faɗin ƙasar.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce cikin jihohin da za su fuskanci hazon sun haɗa da Yobe, Borno, Jigawa, kuma Kano.
“Za a kuma fuskanci gajimare tare da hasken rana a jihohin kudu tare da yanayin hadari a kan yankunan bakin teku,” in ji NiMet.
Ta ce ana sa ran fuskantar hasken rana tare da gajimare a faɗin jihohi da yiwuwar samun tsawa a sassan Edo, Bayelsa, Akwa-Ibom, Delta, Cross River da kuma Rivers nan gaba a yau.
Har ila yau, NiMet ta ce za a samu hazo mai cike da ƙura a jihohin arewa a ranar Asabar.