Masu shirya gasar cin kofin duniya da za a yi a wanna shekarar a kasar Qatar a wannan shekarar, sun kauda tababar da ake da damuwa kan iskar Carbon mai gurbata muhalli.
Kungiyar masu rajin kare muhalli ta Carbon Market Watch, sun ce tasirin da gasar za ta yi ba dan kankani ba ne.
Sun ce bincike ya nuna an kirga adadin iskar carbon da filayen wasanni bakwai da za a buga tamaular a ciki za su fitar, ana kuma son ganin hakan ba wai a lokacin gasar cin kofin duniyar kadai ba.
Wannan na kunshe cikin rahoton da kungiyar ta fitar, wadda duk da haka ta ke nuna tababa kan cimma wanna mataki. A cewar BBC.
Sai dai masu shirya gasar ta Qatar 2022, sun yi watsi da zarge-zargen, sun kafe cewa suna aiki tukuru domin ganin an yi gasar ba tare da gurbatacciyar iskar carbon ba.