fidelitybank

Za a wallafa sakamakon zaɓen gwamnan Bayelsa da Imo tare da Kogi daga rumfar zaɓe – INEC

Date:

Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC, ta ce za a wallafa sakamakon zaɓe daga rumfunan zaɓen gwamna a jihar Bayelsa da Kogi da kuma Imo a shafin intanet na hukumar da ake wallafa sakamakon zaɓe.

Hukumar zaɓen ta sanar da hakan ne a wata sanarwa da fitar a ranar Alhamis.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ya yi alƙawarin samar da yanayi na bai ɗaya ga dukkan ƴan takara.

Ya ce hukumar ba ta goyon bayan wani ɗan takara a zaɓen gwamnan da za a yi a jihohin Bayelsa da Imo da kuma Kogi.

Ya kuma yi alƙawarin shirye-shiryen ma’aikatan hukumar, yana mai cewa, sun dage da tabbatar da cewa jami’an sun isa wurin zaɓen suna jiran masu kaɗa kuri’a maimakon masu kaɗa kuri’a su je suna jiran isowarsu.

Sanarwar ta ce “Wannan shi ne karo na farko a tarihin mu da ake gudanar da waɗannan zaɓuka a rana guda a faɗin shiyoyin siyasar ƙasar guda uku da suka haɗa da jihar Kogi da ke arewa ta tsakiya, da Imo da ke kudu maso gabas, da kuma Bayelsa da ke kudu maso kudu.”

INEC ta ce ta kammala tura kayan zaɓe da suka haɗa da na’urar tantance masu zaɓe (BVAS) da kuma sauran muhimman kayayyaki.

national tribune newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An samu fashewar wani abu a kamfanin ƴan Chana a Kano

An samu fashewar wani abu a Kamfanin Ƙarfe na...

Ma’aikacin kamfani ya kashe abokin aikinsa a Kano

Rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta ya...

Kotu ta ɗaure Matashin da yake tare titi a Kano da sunan barƙwanci

Kotun majistire da ke unguwar Nomansland a Kano, karkashin...

Bayan kashe Soja yanzu haka an kama ƴan Daba 398 a Kaduna

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna, ta sanar da kama...

Shettima zai san makomarsa bayan taron APC na ƙasa – Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa, sai bayan babban...

Kotu ta ɗaure Matashin da ya shiga ɗakin kwanan Ɗalibai Mata a Kano

Babbar Kotun Shariʼar Musulunci da ke Kofar Kudu a...

Ban gudu daga PDP ba – Namadi Sambo

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Mohammed Namadi Sambo, ya ƙaryata...

Da yuwar Sojojin mu za su shiga yaƙi don tallafa wa Isra’ila – Trump

Rundunar sojin Isra'ila IDF ta ce ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta kai hari cibiyoyin ƙera nukiliyar Iran

Yayin da aka shiga rana ta shida na yaƙi...

Najeriya za ta kwashe ƴan ƙasarta dake zaune a Iran da Isra’ila

Gwamnatin tarayya ta ce, tana kammala shirye-shiryen gaggawa domin...

Makami mai Linzami ya faɗa kan cibiyar tattara bayanan sirrin Isra’ila

Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran ta ce, ƙasar...

Iran ta ƙaddamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila

Rundunar sojin Isra'ila ta ce, Iran ta ƙaddamar da...
X whatsapp