Ministar Al’adu a Birtaniya Michelle Donelan ta yi gargadin cewa za a iya samun dogayen layuka fiye da yadda aka yi tsammani don ganawa da gawar Sarauniya Elizabeth II a babban zauren Westminster.
Ta ce akwai yiwuwar samun dogayen layuka na dubban masu ta’aziyya, da ka iya shafe awa 30 a kan layi.
A kan haka ta gargadi al’umma da su shirya jure wa tsayuwa ta tsawon awanni a kullum, su kuma shirya jure wa yanayi.
Sai dai ta ce ”Gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa ta tabbatar jama’ar da za su yi balaguro zuwa London ba su samu matsala ba.”
Ms Donelan ta ce sama da mutum 1,000 ne a kullum za su kasance a inda jama’a suka yi layi don su taimaka masu.
Ta kara da cewa kamfanonin Tate Modern da Shakespeare Globe za su haska ofisoshinsu da ke London da hoton Sarauniya Elizabeth, sannan shaguna za su raba abin sha ga jama’a.
Bugu da kari an tanadi ban-daki guda 500 a kan hanyar da ke sa zauren na Westminster don biyan bukatar jama’a.