Wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya ce zai dauki shekara goma sha hudu kafin a iya kwashe dumbin baraguzan da suka hada da bama-bamen da ba su fashe ba, da ke jibge a Gaza sakamakon yakinta da Isra’ila.
Pehr Lodhammar – daga Hukumar Kula da Ma’adanai ta Majalisar Dinkin Duniya – ya ce ana bukatar a kwashe tarkacen da yawansu ya kai tan miliyan talatin da bakwai.
Mista Lodhammar ya ce ba za a iya kiyasta adadin bama-bamen da basu fashe ba wanda ke binne a cikin baraguzan.
Ya ce Ba zai yiwu a yi hasashe ba, amma abin da zan iya cewa shi ne, akalla kashi goma cikin dari na bama-baman da ake harbawa, na iya kin fashewa.


