fidelitybank

Za a samu ambaliyar ruwa a Abuja – FEMA

Date:

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta birnin Tarayya FEMA, ta yi gargaɗin samun ruwan sama mai karfi gaske da zai iya haifar da ambaliya a babbar birnin ƙasar Abuja da wasu jihohin ƙasar a ranakun Asabar da Lahadi.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Juma’a mai ɗauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar Nkechi Isa, ya ce hukumar na gargaɗin ne bayan da hukumar kula da yanayi ta ƙasar ta yi hasashen samun ruwan sama mai ƙarfin gaske haɗe da iska da ambaliya da zaizayewar ƙasa a wasu sassan jihohin Katsina da Kano da Bauci da Plateau da Taraba da kuma Abujan

Hukumar kula da yanayi ta kasar NiMET ta yi hasashen cewa za a samu ambaliya ruwa tare da batsewar koguna da iska mai ƙarfi, da zaizaiyewar ƙasa da walkiya da kuma tsawa.

Hukumar ta NiMET ta yi kira a sauya matsugunai ga al’umomin da suke cikin hatsarin fuskantar ambaliyar, wadda za ta iya lalata dukiyoyi tare da haifar da cutattuka.

Babban daraktan hukumar bayar da agajin gaggawa ta birnin Abuja Dakta Abbas Idriss ya ce hukumar ta sanya jami’anta cikin shirin ko-ta-kwana don fuskantar matsalar.

Haka kuma ya yi kira ga mazauna birnin da su riƙa la’akari da gargadin da hukumar ta fitar, tare da kaucewa yin tuƙi ko tafiya a ƙafa a lokacin da ake tsaka da ruwan sama, tare da kauce wa titunan da ruwan zai iya mamayewa.

Ya kuma nemi jama’a da su yi gaggawar tuntuɓar hukumar idan suna buƙatar taimakon gaggawa daga gareta.

vgn news today 2021

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp