Hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja (FCTA) ta ce, za ta rufe duka tasoshin motar da ke aiki ba bisa ƙa’ida ba, a wani mataki na yaƙi da masu fakewa a matsayin direbobi domin yi wa fasinjoji fashi a mota da aka fi sani da ‘One -Chance’.
Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da manema labarai.
An samu rahotannin yin fashi da garkuwa da mutane a Abuja tsawon makonni, inda mazauna birnin ke cikin fargaba kan ayyukan ’yan ta’addan da ke fakewa da sana’ar haya don kai hari da kuma yi wa mutane fashi.
Gidan talabijin na Channels ta ruwaito cewa Wike ya ce hukumar FCTA ta kafa rundunar hadin gwiwa kan laifukan da suka shafi kan iyakoki, tare da mai da hankali kan magance ‘yan fashi da makami.
Ministan ya danganta ƙaruwar aikata laifukan da tasoshin motan da ke aiki ba bisa ka’ida ba da kuma gine-ginen da ba a kammala ba waɗanda ke zama mafakar ɓata-garin.
Ya ƙara da cewa, babban birnin tarayya Abuja a tsakiyar jahohin Neja da Kogi da Nasarawa da kuma Kaduna, inda ake fama da matsalar ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane.
Mista Wike ya ce, akwai buƙatar rushe gine-ginen da ba a kammala ba da masu laifi ke amfani da su, domin fatattakar ɓata-garin.
Ministan ya jaddada muhimmancin yin la’akari da illolin tsaro a yayin da ake magance matsalolin da suka shafi tasoshin mota ba bisa ka’ida ba.


