Bayan yawan ƙwallaye da aka zura a raga, a yau za a kawo ƙarshen gasar da aka ƙwashe kusan wata guda ana gudanarwa.
Inda za a ɓarje gumi tsakanin Najeriya da mai masaukin baƙin gasar, Ivory Coast, domi samun kambin Zakarun Afirka.
Tawagar Super Eagles ta Najeriya na fatan ɗaukar kofin a karo na huɗu a fafatawar da za a yi a birnin Abidjan, yayin da a nata ɓangare Ivory Coast ke fatan lashe kofin a karo na uku bayan na 1992 da 2015.
Kungiyoyin za su yi gumurzu ne a karo na biyu, a cikin wannan gasa da Ivory Coast ke karɓar bakunci, kwana 24 bayan Ivory Coast ta sha kashi a hannun Najeriya a wasan cikin rukuni.
Tawagar Ivory Coast ita ce ƙungiyar da ke karɓar baƙuncin gasar ta farko da ta taɓa kai wa wasan ƙashe a gasar, tun bayan Masar a 2006, yayin da biyar daga cikin masu masaukin baki shida da suka kai wasan ƙarshe suka lashe kofin, in ban da Najeriya a shekarar 2000.
Ba a dai taɓa doke Najeriya ba, tun fara gasar, kuma a halin yanzu ita ce babbar kungiya a cikin tawagogin biyu da suka kai wasan ƙarshe.
Najeriya ce ƙasa ta shida a iya murza leda a Afirka, kuma ta 42 a duniya, yayin da Ivory Coast ke matsayi na 8 a Afirka kuma ta 49 a duniya.
Najeriya – wadda ke fatan lashe kofinta na farko tun shekarar 2013 – ta kai wasan na ƙarshe ba tare da shiga wani matsi ba wasanninta, bayan da ta samu maki bakwai a matakin rukuni, sannan ta doke Kamaru da Angola da kuma Afirka ta Kudu a zagaye sili ɗaya ƙwale.
Ita kuwa ivory Coast bayan kashin da ta sha a hannun Najeriya a matakin rukuni, ta sake shan kaye a hannun Equitorial Guinea da ci hudu da nema, sannan ta tsallake rijiya da baya a matsayin ta uku mafi kyau.
A lokacin da suka shiga zagaye na 16, sun sake fitowa ƙarfi, inda suka fitar da Senegal mai rikƙe da kofin gasar sannan suka doke Mali, kafin su doke Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango a wasan kusa da na ƙarshe.
Bayan ƙoƙari da mamakin da ƙungiyar ta bayar a gasar, a yanzu fatanta shi ne lashe kofin a wasan da za a buga gaban ‘yan kallo kusan 60,000 a birnin Abidjan.
Tuni dai shirye-shirye suka yi nisa a wasan da za a buga da misalin ƙarfe 8:00 na dare agogon ƙasar.