Babbar kotun jihar Kano, ta yanke wa wani matashi dan shekara 19 mai suna Ibrahim Khalil, hukuncin kisa ta hanyar rataya, bisa samunsa da laifin kashe dan uwansa Ahmad Ado mai shekaru biyar.
Mai shari’a Usman Naabba ya samu Khalil da laifin yin garkuwa da mutane da kuma kisan kai.
A cewar Na’abba, mai gabatar da kara ya tabbatar da tuhumar da ake yi masa ba tare da wata shakka ba, sakamakon haka ta yanke wa wanda ake tuhuma hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari bisa samunsa da laifin yin garkuwa da mutane da kuma kisa ta hanyar rataya saboda kisan kai.
Lamido Sorondinki, lauya mai shigar da kara, ya shaida wa kotun cewa, Khalil ya aikata laifin ne a shekarar 2019 a Karkasara Quarters a cikin birnin Kano.