fidelitybank

Za a rataye ɗan Damben da ya kashe matarsa a Adamawa

Date:

Wata babbar kotu a jihar Adamawa, ta yanke wa wani dan damben gargajiya hukuncin kisa ta hanyar rataya, saboda ya kashe matarsa.

Thank-You Grim, fitaccen dan damben gargajiya ya fito ne daga yankin Silli a karamar hukumar Guyuk a jihar.

Da yake yanke hukuncin mai shari’a Nathan Musa, ya ce masu shigar da kara sun gamsar da kotun cewa, Grim ya aikata laifin don haka kotun ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Masu shigar da karar sun ce sai da mutumin da ake karar ya jefo matar kasa kafin ya yi amfani da tabarya ya doka mata aka abin da ya janyo mutuwarta a 2018.

Jaridar Daily Trust ta ce, ma’auratan dama ba sa tare tun a farkon shekarar saboda sabanin da suka samu.

Kuma lamarin ya auku ne bayan da matar ts samu wani da za ta aura a nan ne ta nemi takardar saki daga wajen tsohon mijin nata.

Amma maimakon ya aika mata takardar, sai ya gayyace ta gidansa a kan ta je ta karbi takardar sakin, ko da ta je sai ya nemi su sasanta amma ta ki.

Anan ne kuma rikici ya kaure tsakaninsu sai duka ya biyo baya daga nan kuma sai ya rarumo tabarya ya kwada mata a kanta.

uanguard news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp