fidelitybank

Za a mika gawar Atsu Ghana daga Turkiyya

Date:

Nan gaba kaɗan ne a yau za a mayar da gawar ɗan wasan Ghana Christian Atsu zuwa gida daga Turkiyya inda ya mutu sakamakon girgizar ƙasar da ta afka wa wani yanki na ƙasar.

A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Ghana ta fitar ta ce gwamnatin ƙasar na gudanar da shirye-shirye domin tarbar gawar ɗan wasan.

Ana sa ran isar gawar zuwa ƙasar da misalin ƙarfe 7:40 na maraicen ƙasar kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Gawar Atsu za ta isa Ghana ne a jirgin Turkish airlines tare da rakiyar jakadan Ghana a Turkiyya da kuma iyalan ɗan wasan.

Sanarwar ta ce gwamantin ƙasar tare da hukumar wasannin ƙasar ne za su tarbi gawar a filin saukar jiragen sama na ƙasa-da-ƙasa da ke Kotoka.

Daga ƙarshe sanarwar ta miƙa sakon ta’aziyya ga iyalan ɗan wasan tare da addu’ar neman gafara a gare shi.

Atsu dai ya rasu ne sakamakon girgizar ƙasar da ta afka wa Turkiyya da Syria kusan makonni biyu da suka gabata.

A ranar Asabar ne wakilin ɗan wasan ya bayyana gano gawarsa a ƙarƙashin ɓaraguzan gidansa kwaniki 13 bayan afkuwar girgizar ƙasar.

Atsu mai shekarar 31 ya yi wasanni a ƙungiyoyin Chelsea da Newcastle.

latest news 
in nigeria today 2021 punch

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp