Gwamnatin jihar Neja na shirin tsawaita hutun haihuwa ga ma’aikatan jihar daga watanni uku zuwa shida.
Ma’aikatan gwamnati maza da matansu suka kwanta kuma ana neman hutun mako biyu na haihuwa.
Dokta Mohammed Gana, babban sakatare na ma’aikatar lafiya ta jihar Neja ne ya bayyana hakan a ranar Talata, yayin bikin kaddamar da makon shayar da jarirai ta duniya a jihar.
Ya kuma tabbatar da cewa, an kai matakin da ake na bitar hutun haihuwa a Jihar.
Babban Sakataren ya bayyana cewa, gwamnati na kokarin samar da tsarin tallafi wanda zai tabbatar da cewa, aiki kowane irin aiki ba zai raba iyaye mata masu shayarwa da jariransu ba.