Hukumar samar da ruwan sha da tsaftar muhalli RUWASA ta gwamnatin jihar Kano, tare da hadin gwiwar wata kungiya mai zaman kanta mai suna Swiss Mark-Sawa, sun dauki matakin magance matsalar karancin ruwan sha a kauyukan jihar.
A cewar shugaban hadin gwiwa da kirkire-kirkire na kamfanin Swiss Mark na kasar Denmark a Najeriya, Amidele Oshidele, ya ce, an gudanar da aikin ne domin tabbatar da cewa, al’ummomin Najeriya sun samu ruwan sha ta hanyar da ta dace.
Oshidele ya ce, “aikin zai raba buhunan Sawa (Solar SACK) 2,000 ga kananan hukumomin jihar guda tara: Minjibir, Gwarzo, Sumaila, Wudil, Gwangwazo, Warawa, Bichi, Rano da Bagwai.
“Buhun na iya tsarkake ruwa har lita 2,000, kuma ya na daukar sa’o’i hudu kafin ya tace shi ta hanyar amfani da hasken rana, yawanci ya na aiki ne ga gurbatattun halittu kamar kwayoyin cututtuka.”
“Muna gudanar da wannan aikin gwaji ne tare da tallafin ma’aikatar albarkatun ruwa kuma za mu raba buhu 2,000 ga kananan hukumomin da suka fi fama da cutar kwalara a bara. In ji Oshidele.