Babban hafsan rundunar sojin sama ta Najeriya Air Marshal Hassan Abubakar, ya ce nan ba da jimawa ba za a kawo wa rundunar sabbin jiragen yaƙi 18 da ta saya don bunƙasa ƙarfin ayyukanta.
Air Marshal Hassan Abubakar, ya bayyana hakan ne lokacin ziyarar ƙaddamar da wasu ayyukan rundunar a birnin Fatakwal na jihar Rivers.
Ya ce 12 daga cikinsu jirage ne masu saukar-ungulu na kai hare-hare, waɗanda ta saya daga Amurka, sai kuma sauran wasu shida da ta saya daga Turkiyya, waɗanda za a kai su Najeriya cikin watan Satumba mai zuwa.
Makonni biyu da suka gabata ne dai wani jirgin soji ƙasar ya faɗi a jihar Neja ɗauke da sojojin da suka jikkata a wani kwanton-ɓauna da ‘yan bindiga suka yi musu a jihar.


