Rauf Aregbesola, ministan harkokin cikin gida, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa, za’a kawo karshen rashin tsaro a kasar nan a watan Disamba.
Aregbesola ya bayar da wannan tabbacin ne a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Abuja.
A cewar Aregbesola, Buhari ya ce ba zai bar kasar nan ba tare da takaitawa da magance matsalolin tsaro yadda ya kamata ba.
Ministan ya ce Buhari ya baiwa jami’an tsaro wa’adin watan Disamba domin su dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a dukkan sassan kasar nan.
“Ya ba da wa’adin kawo karshen irin wannan barazana ga tsaro na rayuka da dukiyoyi kafin watan Disamba.
“Na yi imanin cewa babu wanda ke hutawa a dukkan hannun gwamnati tare da wanzar da doka da oda, tabbatar da tsaro da kawar da barazana.
“Muna kan haka, kuma a matakin farko, dole ne mu tambayi kanmu cewa, mulki shine tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.
“Za mu kawar da duk matsalolin rashin tsaro nan da Disamba.
“Idan ka dubi yadda al’amura ke gudana a Najeriya, zan gaya maka cewa an samu ci gaba da dama a cikin shekaru,” in ji shi.
Aregbesola ya tuna cewa kafin shekarar 2015 ‘yan Najeriya na zaune da bama-bamai a ko’ina.
Ministan, ya ce gwamnati ta kawar da abubuwan da ke faruwa na bama-bamai, kuma ‘yan Najeriya ba su da irin wannan fargaba.