Wata kotun shari’a da ke zamanta a Ningi karamar hukumar Ningi a jihar Bauchi ta yanke wa wasu mutum uku hukuncin kisa ta hanyar jifa.
An same su da laifin yin luwadi da madigo wanda Musulunci bai yarda da shi ba.
Wadanda aka yankewa hukuncin sune: Abdullahi Abubakar Beti mai shekaru 30, Kamilu Ya’u mai shekaru 20 da Mal. Haruna shekara 70, bisa tanadin sashe na 134 na dokar hukunta manyan laifuka ta Jihar Bauchi na shekarar 2001 da kuma tanadin Fiquhussunah Jizu’i mai lamba 2 a shafi na 362.
An fara shari’ar wadanda aka yanke wa hukuncin ne a ranar 14/6/2022 lokacin da ‘yan kungiyar Hisbah Vanguard da ke aiki a karamar hukumar Ningi ta hannun Adamu Dan Kafi, suka gurfanar da wadanda suka aikata laifin guda uku, Abdullahi Abubakar Beti, Kamilu Ya’u da Mal Haruna a gaban kotun Shari’a.
Hukumar Hisbah Vanguard ta shaida wa kotun cewa, an kama mutanen uku ne da laifin yin luwadi a kauyen Gwada da ke karamar hukumar Ningi.
Bayan sauraron karar da ake tuhumarsu da laifukan da ake tuhumarsu da shi, Alkalin Shari’a, Munka’ilu Sabo Ningi, ya dage sauraron karar zuwa ranar Laraba 29/6/2022 domin yanke hukunci.
A yayin da yake yanke hukuncin kotun bayan sauraron bayanan shaidu da kuma amincewa da laifukan da ake tuhumar mutanen uku, alkalin kotun, Munka’ilu Sabo Ningi, ya yanke musu hukuncin kisa ta hanyar jifa.