fidelitybank

Za a kammala aikin titin Abuja zuwa Kano a naira biliyan 280 cikin wata 14 – Minista

Date:

Ministan ayyuka Sanata David Umahi, ya ce, gwamnati za ta rinƙa biyan kamfanin Julius Berger naira biliyan 20 a duk wata, domin kammala aikin sashen kilomita 82 na titin Abuja zuwa Kano, tsawon wata 14 nan gaba.

Ministan wanda ya bayyana haka a yayin ganawa da kamfanin domin sake duba dukkanin kwangilolin tituna da kamfanin ke yi, ya nuna damuwarsa kan ƙarancin kuɗi don kammala ayyukan da gwamnatinsu ta gada.

A game da titin na Abuja zuwa Kano, ministan ya buƙaci kamfanin da ya tsaya a kan aikin ɓangare ɗaya na titin, bayan ya kammala sai ya koma ɗaya ɓangaren.

Ministan ya kuma umarci kamfanin na Berger da cewa nan da mako uku ya cike dukkanin ramukan da ke titin da duwatsu domin magance matsalar rashin kyawun hanyar da masu motoci ke fama da ita.

Kamfanin ya kasa ragowar aikin gida huɗu kuma ya yi alƙawarin kammalawa duka cikin wata 14.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a wata sanarwa da, jami’in yaÉ—a labarai na ministan, Orji Uchenna Orji, ya fitar, ya ce ayyukan titunan sun haÉ—a da na Abuja zuwa Kaduna zuwa Zaria zuwa Kano, da kashi na biyu na titun Legas zuwa Ibadan da Gadar Anacha ta biyu, sai kuma gadojin da ke jihar Legas – Gadar Third Mainland, da Gadar Iddo da kuma Gadar Carter.

sani ahmad

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp