Kamfanin mai na Najeriya, NNPCL ya ce a cikin watan nan ne za a kammala gwajin matatar mai ta Fatakwal da ke kudancin ƙasar don ci gaba da aikin tace mai bayan shafe shekaru biyar a rufe.
Kakakin kamfanin Femi Soneye ya ce “nan ba da daɗewa bane za a kammala gwajin matatar don tabbatar da tana aiki yadda ya kamata. Za a kammala a cikin wannan watan.”
Matatar wadda ake inganta ta, za ta soma tace gangar mai 60,000 duk rana kuma kamfanin na NNPCL yana sa ran nan gaba a shekarar, za ta riƙa tace ganga 210,000 ta mai kowace rana.
Matatar man ta Patakwal ɗaya ce daga matatun mai na gwamnati da suka shafe tsawon shekaru a durƙushe wanda kuma a yanzu gwamnatin ke son farfaɗo da ita da nufin kawo karshen dogaron da ƙasar ke yi kan tataccen man da ake shigowa da shi daga wasu ƙasashe.
Ana ganin idan matatar man ta soma aiki, za ta taimaka wajen samuwar man fetur a kasar tare da sauƙaƙa wa ƴan ƙasar wahalhalun da suke fuskanta ta dalilin rashin iya tace man a ƙasar.


