fidelitybank

Za a kafa dokar tilasta yin gwajin cutar Aids kafin aure a Kano

Date:

Hukumomi a jihar Kano sun ce shirye-shirye sun yi nisa, domin kafa dokar da za ta tilasta a waɗanda suke shirin aure yin gwajin cututtuka ciki har da cuta mai karya garkuwar jiki.

Sun ce ɗaukar matakin ya zama wajibi don daƙile bazuwar cutuka tsakanin ma’aurata a jihar Kano.

Dakta Usman Bashir shi ne darakta janar na hukumar yaƙi da cutar HIV ko Sida na jihar Kano ya shaida wa BBC cewa an ɗauki matakin ne domin tabbatar da kare ma’aurata daga yaɗa cutukan da ake iya ɗauka ta hanyar auratayya, da kuma haihuwar ‘ya’yan da ke ɗauke da cutukan da ake iya gada.

Ya kuma ce yawanci cuta mai karya garkuwar jiki ana iya ɗaukarta ne ta hanyar saduwa, ”inda za ka ga mutum na da mata uku, amma daga ƙarshe sai ya auro matar da ke ɗauke da cutar ya kuma zo ya yaɗa wa sauran matan nasa”.

”To hanyar da za a iya kauce wa wannan shi ne a riƙa yin gwaji kafin aure”.

Ya kuma ce dokar gwajin da za a yin ba ta HIV ce kaɗai ba, har da sauran cutukan da za a iya ɗauka ta hanyar saduwa waɗanda su ma ke da illa.

Sauran cutukan da gwajin zai shafa, sun haɗar da cutar ciwon hanta da cutar sikila da cutar da cutar sifilis.

”Za kuma mu haɗa da gwajin shaye-shaye, ta hanyar gwada ƙwaƙwalwar mutum don tabbatarwa da cewa lafiyarsa kalau”, in ji Dakta Usman.

Ya ƙara da cewa an kwashe tsawon shekara bakwai ana fafutikar kafa wannan doka, inda ta riƙa samun tangarɗa a baya, amma ya ce a yanzu dokar ta wuce karatu na biyu a majalisar dokokin jihar.

”Yanzu abin da ya rage shi ne a zauna da masu ruwa da tsaki, ciki har da malaman addini domin yi wa dokar kallon tsakani kafin a sake mayar da ita majalisa don a amince da ita, kafin a kai wa gwamna ya sanya mata hannu ta fara aiki a jihar Kano”.

Ya kuma ce idan batun ya zama doka to za a tanadi hukunci ga duk malami ko limamin da waliyyan da suka ɗaura aure ba tare da takardar gwajin ba.

Dakta Usman ya ce ƙiyasi ya nuna cewa jihar Kano na da masu fama da lalurar cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV kimanin mutum 120,000, to sai dai ya ce kimanin mutum 42,000 ne ke kan magani.

nigerianewstoday

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp