Najeriya na shirin janye jami’an ‘yan sanda masu bai wa manyan jami’an gwamnati tsaro bisa umarnin shugaban kasa, kamar yadda karamar ministar harkokin ‘yan sanda, Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim ta sanar.
Ta bayyana irin kalubalen da rundunar ‘yan sandan ke fuskanta sakamakon rashin kula da su na tsawon shekaru, wanda ke kawo mata cikas wajen sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya dora mata.
A ci gaba da kokarin da shugaban kasa ya yi na ganin an farfado da aikin ‘yan sanda mai inganci, Sulaiman-Ibrahim ta jaddada buƙatar ‘yan sanda su daidaita tare da inganta ayyukansu.
Ta bukaci cikakken nazari kan cibiyoyin horarwa don dacewa da tsarin aiwatar da doka na zamani da ka’idojin ƙasashen duniya.
Ta yi wannan jawabi ne a wani taron kwana biyu da ‘yan sanda suka gudanar a Abuja.
Ta ce ma’aikatar tana da muhimman a wajen “haɓaka da aiwatar da ingantaccen rahoton sake fasalin ‘yan sanda da kuma yin gyaran fuska ga aikin ‘yan sanda, tare da aiwatar da umarnin shugaban ƙasa kan janye jami’an ‘yan sanda daga ayyukan tsaron ƴan siyasa don haɓaka dabarun aikin ɗan sanda na al’umma”.
Wadannan tsare-tsare na da nufin kawo sauyi da inganta harkokin tsaron cikin gida a Najeriya


