Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya sake caccakar kafa ‘yan sandan jihohi.
Da yake wallafawa a shafinsa na X, Sani ya ce akwai yiyuwar ‘yan sandan jihohi su yi arangama da ‘yan sandan tarayya a wani lamari da ke tsakanin bangarorin gwamnati biyu.
“Idan kana da ‘yan sandan Jiha, ta haka ne za su rika yin musayar wuta da ‘yan sandan tarayya, idan aka samu rikici tsakanin Gwamnatin Jihar da Gwamnatin Tarayya,” inji shi.
Tsohon Sanatan ya yi magana ne a kan koma bayan rahotannin da ke cewa Shugaba Bola Tinubu da gwamnonin jihohi na duba yiwuwar bullo da ‘yan sandan jihohi domin magance matsalolin tsaron kasar nan.


