Shugabannin ƙasashen yamma sun yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar a shafe shekara huɗu ana gwabza yaƙi a Ukraine inda suka ce akwai buƙatar a samu agaji mai ɗorewa domin kare ƙasar daga mamayar Rasha.
Firaiministan Birtaniya Boris Johnson wanda ya kai ziyara a Kyiv a ranar Juma’a ya fitar da tsare-tsare huɗu na samar da makamai da kuma bayar da agaji ga tattalin arziki Ukraine.
Mista Johnson ya ce, burin Shugaba Putin na Rasha ba zai tsaya kawai a tarwatsa Ukraine ba kaɗai.
Shugaban sashen siyasa na ƙungiyar NATO, Jens Stoltenberg ya bayyana cewa akwai buƙatar a ci gaba da kai wa Ukraine ɗauki ko da a ce kuɗin da za a kashe suna da yawa idan ba haka ba Mista Putin zai ci gaba da abin da yake yi.
A bidiyon da ya yi na baya-bayan nan, Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya bayyana cewa Rasha ba ta da isassun makamai masu linzamin da za ta iya tarwatsa Ukraine baki ɗaya. In ji BBC.