Mutane bakwai daga cikin tawagar jami’an kula da lafiyar shahararren ɗan wasan kwallon kafa na Argentina Diego Maradona kafin rasuwarsa za su gurfana gaban kotu a yau Talata saboda laifin kisa ba da gan-gan ba.
Maradona ya fara samun sauƙi bayan tiyatar da aka mishi gabanin mutuwarsa sakamakon samun bugun zuciya a shekarar 2020 a lokacin ya na da shekara 60.
Shekara ɗaya bayan hakan, masu gabatar da kara su ka ƙarƙare cewa mutuwarsa abu ne da za a iya guje mawa inda su ka ɗaura laifin kan sakaci.
Tawagar jam’ian kula da lafiyar sun ce Maradona ya ƙi amincewa a bashi kulawa, kuma ya kamata a ce ya zauna a asibitin na tsawon lokaci kafin ya tafi gida bayan tiyatar.
Shari’ar za ta saurari ba’asi daga shaidu fiye da 100, kuma a na sa ran cigaba da shari’ar har watan Yuli.