Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Osun ta tsara gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar a ranar 15 ga Oktoba, 2022.
Shugaban Hukumar, Segun Oladitan, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin ganawa da manema labarai a ofishin OSSIEC da ke Osogbo, babban birnin jihar.
Oladitan ya ce, yana sane da karar da ke kalubalantar yadda aka gudanar da zaben kafin ficewar gwamna mai ci Gboyega Oyetola a watan Nuwamba amma ya ce duk wani mutum ko jam’iyyar da bai ji dadi ba to ya kamata ta bar kotu ta yi aikinta.