Sarki mafi ɗaɗewa a mulkin wani yankin Zamfara, Sarkin Kwatarkwashi a karamar hukumar Bungudu, Alhaji Ahmad Umar (Mai-Kwatarshi), ya rasu yana da shekara 93.
Sarkin ya shafe shekara 61 kan karagar mulki.
Sakataren gwamnati, Alhaji Kabiru Balarabe, ne ya sanar da mutuwar, yana mai cewa sarkin ya rasu ne bayan doguwar jinya.
Balarabe ya ce, za a gudanar da jana’izar sarkin da yammacin wannan Juma’a a fadarsa da ke Kwatarkwashi.
Sultan Abubakar na uku ne ya naɗa sarkin a ranar 17 ga watan Mayun, 1961.