Hukumomi sun ƙaddamar da wani shiri na gina kusan ban-ɗaki dubu biyu a Abuja, domin magance matsalar yin ba-haya a fili ko bainar jama’a.
An ƙaddamar da shirin ne a yau Talata a Abuja inda hukumomin ƙasar suka ce za a ɗauki shekara uku ana gudanar da aikin samar da ban-ɗakin tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyi.
Bugu da ƙari shirin ya kuma ƙunshi samar da tsaftataccen ruwan sha wanda zai taimaka wurin kawar da yaɗuwar cututtuka.
Ministan albarkatun ruwa ya bayyana cewa, suna da niyyar faɗaɗa wannan shirin zuwa jihohi 36 na Najeriya.