Masu amfani da wutar lantarki a jihar Legas na iya fuskantar katsewar wuta daga ranar Litinin, yayin da kamfanin rarraba wutar Lantarki na Najeriya (TCN), zai fara aikin gyare-gyaren a layin wuta na Omotosho zuwa wani yanki na Ikeja West.
A cikin wata sanarwa, TCN ya bayyana cewa hukumar kula da harkokin wutar lantarki ta Najeriya (NERC) da kuma Hukumar tsarin rarraba Wuta ta Ƙasa (NISO) ne suka amince da gyare-gyaren.
“Gyaran zai haɗa da shimfiɗa wasu wayoyi na wutar a layin wutar lantarki na Omotosho/Ikeja wanda aka shirya farawa daga ranar 28 ga Yuli, 2025 zuwa 21 ga Agusta, 2025 daga ƙarfe 8 na safe zuwa 5 na yamma,” in ji sanarwar da shugabar hulɗa da Jama’a na TCN, Ndidi Mbah, ta fitar.
Ta kara da cewa bayan kammala aiki a kowace rana, za a maido da wuta ta wannan layi, kuma sauran layukan zasu ci gaba da aiki domin tabbatar da cewa Legas na samun isasshen wuta.
Haka kuma, kamfanonin rarraba wutar lantarki na Eko da Ikeja sun shaida wa abokan cinikayarsu cewa za a fuskanci “yawan katsewar wuta lokaci-lokaci” a lokacin aikin.