Gwamnatin Tarayya ta ce, za ta fara yi wa ɗaliban jami’o’in ƙasar gwajin shan ƙwayoyi a wani mataki da daƙile yaɗuwar ta’ammalai da ƙwayoyin.
Ma’aikatar ilimin ƙasar tare da haɗin gwiwar hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasar NDLEA ne za su jagoranci aiki, kamar yadda wata sanarwa da hukumar NDLEA ta fitar.
Hakan na zuwa ne bayan ganawar shugaban hukumar NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya da kuma ministan ilimin ƙasar, Olatunji Alausa.
Ɓangarorin biyu sun kuma amince da ɓullo da daftarin koyar da darasin ilimin ta’ammali da ƙwayoyi a makarantun sakandiren ƙasar.
Buba Marwa ya tabbatar wa BBC cewa gwajin ƙwayar zai shafi duka ɗaliban jami’o’in da sabbin da za su shiga.
Yayin da yake jawabi a wajen ganawar, Buba Marwa ya ce za su mayar da hankali ne kan makarantun ƙasar, waɗanda ya ce akwai miliyoyin yara da ke ƙarƙashin kulawar ma’aikatar ilimin ƙasar.
Buba Marwa ya ce rashin daƙile ta’ammali da miyagun ƙwayoyi daga wajen ƙananan yara ya taimaka wajen jefa matasan ƙasar cikin ayyukan ta’addanci da fashin daji da sauran miyagun laifuka.