A yau ne za a fara wasannin nakasassu wato Paralympics a birnin Paris, inda za a lashe lambobin yabo a tseren keke da ninƙaya da table tennis.
A gagarumin bikin buɗɗe wasannin da aka yi a daren Laraba, shugaban kwamitin shirya wasannin ya ce yana son wasannin na bana su kayatar waɗanda suka ƙunshi har da sabbin ƴanwasan da ba a taba gani ba.
Dimbin jama’a ne suka taru domin ganin yanwasa da dama daga sassan duniya.