A yau ne hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta EFFCC, za ta gurfanar da tsohon Akanta Janar na kasar Ahmed Idris a gaban wata babbar kotu a Abuja, domin fara yi masa shari’a kan zargin almundaha da hukumar ke yi masa.
Kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja babban birnin kasar.
Mista Uwujaren, ya ce za a gurfanar da tsohon Akantan tare da wasu mutum uku, bisa zargin sama-da-fadi da kudi sama da naira biliyan 109.
Sauran mutum ukun da ake zarginsa da su, su ne Godfrey Akindele, da Mohammed Usman sai kuma kamfanin Gezawa Commodity Market and Exchange Limited.
Cikin watan Mayun da ya gabata ne dai EFCC ta kama babban Akanta Janar na kasar bayan ya ƙi amsa gayyatar da hukumar ta rinƙa aika masa domin tuhumarsa kan zarge-zargen da ake yi masa, kamar yadda hukumar ta bayyana.