Hukumomi sun ce za a fara kashewa ko kuma amfani da sabbin takardun Naira da Babban Banki CBN ya ƙaddamar a yau Laraba.
Tun farko CBN ya ce sai a ranar 15 ga watan Disamba ne zai fito da kuɗin da aka sauya wa fasali kafin ya sauya shawarar yin hakan a yau.
Takardun kuɗin su ne: N1,000, da N500, da kuma N200.
Shugaba Buhari ne ya jagoranci bikin da aka yi a Fadar Shugaban Ƙasa. A gefe guda kuma akwai Gwamnan CBN Godwin Emefiele da Shugaban hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa, da sauran manyan jami’an gwamnati.
Sai dai wa’adin da CBN ya bayar na daina amfani da tsofaffin kuɗin na ranar 31 ga watan Janairun 2023 na nan daram.