Shugaban ƙungiyar ta IPMAN, ya danganta faɗuwar farashin man fetur ɗin a kan wasu dalilai biyu da suka haɗar da rashin kuɗi da kuma damuna.
Ya ce da ma a al’ada idan damuna ta kankama, manoma ba sa bukatar su sayi mai, akwai kuma rashin kuɗi da kuma rashin amfani da man, don haka dole shi kansa farashin fetur ya karye.
Sai dai duk da cewa Bashir Dan-malan bai bayyana taƙamaiman lokacin da za a fara samun man fetur mai sauƙin a gidajen mai ba, amma ya ce nan ba da jimawa ba mutane za su fara gani.
Danmalam ya ce ana dab da ganin sauyi, saboda ba kowa yake da kuɗin da zai iya siyan mai yanzu ba.
Shugaban kungiyar IPMAN reshen arewacin Najeriya, ya ce hasashen da suka yi tun farko a kan cewa farashin man fetur zai iya kai naira 600 zuwa 700 a lokacin bazara zai iya faruwa ne kawai idan aka fuskanci ƙarancin dala.