Majalisar Dattijai ta yi karatun farko ga wani ƙuduri da ke neman a ci tarar naira 50,000 ga iyayen da suka gaza bai wa ‘ya’yansu ilmin firamare da sakandire.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Majalisar ta kuma buƙaci a riƙa bai wa kowanne yaro abinci kyauta a Najeriya.
Ƙudurin wanda Sanata Orji Kalu ya gabatar mai taken ‘Dokar ba da ilmi kyauta kuma dole a matakin farko ga kowa ta 2004, Sashe na 2, na cewa kowacce gwamnati a Najeriya ta samar da ilmin bai ɗaya kyauta kuma dole ga duk yaron da ke cikin shekarun shiga firamare da ƙaramar sakandire.
Ƙudurin dokar ya kuma ce “Duk iyaye su tabbatar da cewa yaronsu sun halarta kuma sun kammala ilmin firamare da na ƙaramar sakandire ta hanyar ƙoƙartawa wajen tura su makarantar firamare da kuma ta sakandire”.