fidelitybank

Za a fara biyan ƴan NYSC alawus ɗin 77,000 daga watan Febrairu

Date:

Shugaban hukumar kula da matasa masu yiwa ƙasa hidima NYSC, Birgadier Janar Yushau Ahmed ya ce za a fara biyan matasan alawus din naira 77,000 daga watan Fabrairun 2025.

Shugaban hukumar ya faɗi hakan ne a jihar Katsina a lokacin da yake yi wa sabbin matasan da aka ɗauka na rukunin ‘C’ jawabi, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Yushau ya tabbatar da cewa ƙarin alawus ɗin na cikin kasafin kuɗin ƙasar na shekarar 2025 kuma zai fara aiki ne da zarar an amince da kasafin kuɗin.

“Wannan watan na Janairu ya riga ya ƙare, amma da zarar an amince da kasafin kuɗin a watan Fabrairu mai kamawa, za ku fara karɓar naira 77,000 a maimakon 33,000 da ake biya yanzu,” in ji shi.

Ya kuma tabbatar wa matasan cewa ba za a aika su yankunan da babu tsaro ba.

A ranar 25 ga watan Satumban bara ne dai gwamnatin ƙasar ta sanar da yi wa ƴan bautar ƙasa ƙari a alawus ɗin su zuwa naira 77,000 da zai soma aiki daga watan Yulin da ya gabata, wanda aka yi saboda ƙarin mafi ƙanƙantar albashi da gwamnatin ta yi.

the nation newspaper nigeria today latest

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp