Ministan Sufurin Jiragen Kasa, Mu’azu Jaji Sambo, ya ce, suna sa rai nan ba da jimawa jigila za ta dawo tsakanin Abuja zuwa Kaduna.
Ya bayyana haka ne ranar Juma’a a Abuja, babban birnin kasar.
Ministan ya fadi dalilin da ya sa fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da aka ceto ba su je Abuja domin ganawa da gwamnati ba.