Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci, kuma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar na III, ya ce za a dauki shekaru masu yawa kafin Arewa maso Yamma ta shawo kan ‘yan ta’adda da rashin tsaro.
Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a wajen taron zaman lafiya da tsaro a yankin Arewa maso yamma da aka gudanar a jihar Katsina.
Ya ce, kamata ya yi a kalubalanci ‘yan tada kayar baya saboda duk kowa ya san illar su a zahirance.
Ya kuma ce, za a ɗauki shekaru da yawa kafin a fita daga cikin wannan kangin.
Sarkin ya bayyana shirin sarakunan gargajiya na yin hadin gwiwa da jami’an tsaro da gwamnonin Arewa, domin ceto yankin daga dimbin matsalolin ‘yan fashi da tayar da kayar baya.