Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya aike da ta’aziyyarsa ga iyalai da ‘yan uwa da abokai da mabiyan fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Abubakar Giro Argungu, wanda ya rasu ranar Laraba.
Shugaba Tinubu ya bayyana mutuwar malamin da babban rashi ga ƙasar baki ɗaya, sakamakon irin gudunmowar da yake bayarwa wajen yaɗa ilimin addinin musulunci da gyaran tarbiyya ga ƙasar.
“Za a daɗe ana tunawa da Sheikh Giro Argungu a ƙasarnan sakamakon shekarun da ya ɗauka yana yaɗa ilimin addini a ƙasar”, in ji Tinubu, cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ya fitar.
Ayyukan Malamin ta hanyar ƙungiyar JIBWIS, inda ya kasance shugaban kwamitin gudanarwa na ƙungiyar – sun taimaka wajen ilimantar da matasan Musulmin ƙasar.
Tinubu ya ce, za a daɗe a na tuna malamin kan irin tsoron Allah da tawali’unsa da yadda yake kiran shugabanni a matakai daban-daban wajen sauke nauyin talakawa da ya rataya a wuyansu.
Daga ƙarshe shugaban ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalai, da gwamnatin jihar Kebbi da musulman Najeriya, kan wannan babban rashi, tare da yin addu’ar samun gafara shehin malamin


