Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya ce yakin da kasarsa ke yi a Gaza da ya shafe shekara guda zai ci gaba da gudana, matsawar kasarsa na ci gaba da fuskantar barazana.
Ya ce ba abu ne mai yiwuwa a dakatar da hare-haren da kasarsa ke kaiwa Gaza da Lebanon da sauran yankunan gabas ta tsakiya da suke yaki da su ba.
Ya ce wanan wani nauyi ne da ya rataya a wuyanmu, kuma ba za mu dakata ba, har sai mun cika aikin.
Yana magana ne a wani jawabi da ya gabatarwa yan kasar bayan taron zagayowar ranar 7 ga watan Oktoba, da Hamas ta kai hari Isra’ila.
A gefe guda Isra’ilar ta ci gaba da yin luguden wuta a birnin Beirut, na Labanon, yayin da a nata bangaren, kungiyar Hezbollah ta harba rokoki sama da dari zuwa Isra’ila jiya Litinin kadai.


