Kotun Kolin Nza ta ci gaba da zaman sauraron ƙarar da wasu gwamnonin jihohi suka kai gwamnatin tarayya kan buƙatar ƙara wa’adin amfani da tsofaffin kuɗi.
A ranar 22 ga watan Febrairu ne, Kotun ta ɗage zaman sauraron ƙarar har zuwa yau 3 ga watan Maris ɗin 2023.
Tun farko gwamnatin tarayya ta ayyana ranar 31 ga watan Janairun 2023 a matsayin ranar da za a daina amfani da tsofaffin takardun kuɗi na naira 1,000, da 500, da kuma 200.
Sai dai daga baya shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya amince da ƙara wa’adin zuwa 10 ga watan Fabarairu