Babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Abuja, ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar shugaban ƙungiyar dan aware na IPOB mai rajin kafa ƙasar Biafra, Nnamdi Kanu, har zuwa Laraba.
Kotun ta ce, ta ɗage shari’ar ne domin baiwa lauyoyin da ke kare Nnamdi Kanu damar yin nazari kan sababbin tuhume-tuhume 15 da gwamnatin ƙasar ke yi masa.
Tun da farko, Nnamdi Kanu bai amsa tuhume-tuhumen ba, kuma bai ce bai amince da su ba, bayan an karanto masa su.
Lauyoyinsa sun shaida wa kotun cewa, wanda su ke karewa ba zai iya cewa komai ba, har sai sun yi nazarin tuhume-tuhumen.
A ranar Litinin ne gwamnatin Najreriy ta sake gabatar da sababbin tuhume-tuhume 15 kan Nnamdi Kanu, bayan akwai wasu guda bakwai da aka gabatar masa.