Nan da wani ɗan wani lokaci ne a yau Alhamis Fafaroma Francis zai jagoranci jana’izar wanda ya gada, Benedict na 16 a fadar Vatican.
Tuni dubban jama’a suka fara cika dandalin St Peter’s domin addu’a ga marigayi tsohon Fafaroman, wanda ya rasu a jajiberin sabuwar shekara yana da shekara 95 a duniya.
Shekara 10 bayan saukarsa daga mukamin shugaban ɗarikar Katolika na duniya, saboda rashin koshin lafiya.
Bayan jana’izar ne za a binne shi a wani ɗaki na ƙarƙashin Cocin St Peter’s ɗin, wanda hubbare ne na fafaroma sama da 90 da suka gabace shi