Ƙwararru kan harkokin shari’a sun ce tuhumar ba za ta hana Trump sake tsaya wa takarar shugaban ƙasa ba.
A wani saƙo da ya wallafa a shafin sada zumuntarsa na Truth Social ranar Alhamis, Mista Trump ya ce bai aikata wani laifi ba kuma an ba shi sammaci don ya bayyana a wata kotun tarayya da ke Maimi a jihar Florida ranar Talata, inda za a kama shi kafin ya ji tuhume-tuhumen da ake yi masa.
“Ban taɓa tunanin abu ne mai yiwuwa wani abu mai kamar wannan zai iya faruwa ba ga wani tsohon shugaban Amurka ba,” ya rubuta.
Ya ƙara da cewa: “Haƙiƙa wannan rana ce mai cike da baƙin tarihi ga Amurka. Muna cikin ƙasar da take komawa baya cikin sauri, amma tare (da ku), za mu sake Mayar da Amurka Gawurtacciyar Ƙasa.”
Lauyan Mista Trump, Jim Trusty, ya shaida wa CNN cewa tsohon shugaban ya samu cikakkun bayanai game da tuhume-tuhumen a cikin takardar sammaci.
A cewarsa, tuhume-tuhumen sun haɗar da na haɗa baki da kalaman ƙarya da yi wa shari’a tarnaƙi, da kuma riƙe wasu bayanan sirrin ƙasa ba bisa ƙa’ida ba a ƙarƙashin dokar leƙen asiri.
Ma’aikatar Shari’a (DOJ) dai ta ƙi cewa uffan kuma ba a fitar da tuhumar a bainar jama’a ba.