Kungiyar ƙasashe bakwai masu ƙarfin tattalin arziƙi ta G7 ta amince ta yi amfani da kadarorin Rasha da aka dakatar don tara dala biliyan 50 (£39bn) ga Ukraine wajen taimaka mata yaƙar sojojin Rashan da suka mamaye ƙasar.
Shugaban Amurka Joe Biden ya jaddada matakin a matsayin wani sako mai karfi ga Rasha, wadda ta yi ta yi barazanar ɗaukar matakan ramuwar gayya “mai raɗaɗi”.
A taron G7 da aka yi a Italiya, shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky da Biden sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyar tsaro ta tsawon shekaru 10, inda za ta ba da taimakon sojan Amurka ga Ukraine.
Yarjejeniyar dai na da nufin bunƙasa karfin tsaron Ukraine, da karfafa masana’antar tsaronta, da kuma tallafa mata wajen farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar.
Ƙungiyar G7 da Tarayyar Turai sun dakatar da dala biliyan 325 na kadarorin Rasha bayan mamayewar da ta yi wa Ukraine a shekarar 2022, inda suke samar da dala biliyan uku a duk shekara a matsayin riba.
Ana sa ran samun kudaɗen nan da ƙarshen shekara, inda za su ba da rance na dogon lokaci ga ƙoƙarin yaƙi da farfaɗo da tattalin arziƙin Ukraine. A cewar BBC.