Ministan sufuri, Sanata Sa’idu Alƙali, za a bai wa umarnin shugaban ƙasa muhimmanci na amincewa da ya yi a duba yiwuwar ƙarawa ma’aikatan jirgin ƙasa albashi.
Ya ce zai yi duk mai yiwuwa wajen bunƙasa jindadin ma’aikatar jiragen ƙasa na Najeriya, sannan a kyautata yanayin aikinsu.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kai hedikwatar hukumar da ke Ebute-Meta a Legas.
A cewarsa wannan wata ziyara ce domin ganin yadda ayyukan hukumar suke gudana da kuma nisan da aka yi a ayyukan da take kan yi, yana buga misali da aikin dogo na Legas zuwa Ibadan da na Kano zuwa Maraɗi.


